Matthew 28

Tashin Matattu

1Bayan ranar Asabbaci, da sassafe, a ranar farko ta mako, Maryamu Magdalin tare da ɗaya Maryamun, suka je don su ga kabarin.

2Sai aka yi wata babbar girgizar ƙasa. Don wani malaʼikan Ubangiji ya sauka daga sama, ya je kabarin, ya gungurar da dutsen, ya kuma zauna a kai. 3Kamanninsa yana kama da walƙiya, tufafinsa kuma fari fat kamar dusan ƙanƙara. 4Masu gadin kabarin kuma suka ji tsoro ƙwarai, suka yi rawan jiki, suka zama kamar matattu.

5Malaʼikan ya ce wa matan, “Kada ku ji tsoro, domin na san cewa kuna neman Yesu wanda aka gicciye ne. 6Ai, ba ya nan, ya tashi kamar yadda ya faɗa. Ku zo ku ga inda ya kwanta. 7Sai ku tafi da sauri ku gaya wa almajiransa cewa, ‘Ya tashi daga matattu, ya kuma ya sha gabanku zuwa Galili. Can za ku gan shi.’ Ga shi na faɗa muku.”

8Sai matan suka bar kabarin da hanzari, da tsoro, sai dai cike da farin ciki, suka tafi a guje don su gaya wa almajiransa. 9Kwaram, sai ga Yesu ya gamu da su, ya ce, “Gaisuwa.” Sai suka zo kusa da shi, suka rungumi ƙafafunsa, suka yi masa sujada. 10Sai Yesu ya ce musu, “Kada ku ji tsoro, ku tafi ku gaya wa ʼyanʼuwana, su tafi Galili. A can za su gan ni.”

Rahoton Masu Gadi

11Yayinda matan nan suna cikin tafiya, sai waɗansu daga cikin masu gadin suka shiga gari, suka ba wa manyan firistoci labarin duk abin da ya faru. 12Da manyan firistoci da dattawa suka taru, sai suka ƙulla wata dabara, suka ba wa sojojin kuɗi mai yawa. 13Suka ce musu, “Ku, za ku ce, ‘Almajiransa ne sun zo da dare suka sace shi, lokacin da muke barci.’ 14In wannan labari ya kai kunnen gwamna, za mu lallashe shi, mu kuma kāre ku daga duk wata wahala.” 15Sai sojojin suka karɓi kuɗin, suka kuma yi kamar yadda aka umarce su. Wannan labarin kuwa shi ne ake bazawa koʼina a cikin Yahudawa, har yǎ zuwa yau.

Babban Umarni

16Saʼan nan almajiransa goma sha ɗaya, suka tafi Galili, suka je dutsen da Yesu ya gaya musu. 17Da suka gan shi, sai suka yi masa sujada, amma waɗansu suka yi shakka. 18Sai Yesu ya zo wurinsu, ya ce, “An ba ni dukan iko a sama da kuma ƙasa. 19Saboda haka ku tafi, ku mai da dukan alʼumman duniya su zama almajiraina, kuna yi musu baftisma a cikin
Ko kuwa cikin; dubi Ayy Man 8.16; 19.5; Rom 6.3; 1Kor 1.13; 10.2 da Gal 3.27.
sunan Uba, da na Ɗa, da na Ruhu Mai Tsarki,
20kuna kuma koya musu, su yi biyayya da duk abin da na umarce ku, kuma tabbatacce, ina tare da ku kullum, har ƙarshen zamani.”

Copyright information for HauSRK